Dubban mutane ne suka tsallaka zuwa cikin Columbia daga kasar Venezuela a jiya Asabar domin sayen abinci da kayan magunguna, bayan da shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya ba da umurni a bude kan iyakar kasar da Colombia, wacce ta kwashe wata hudu a rufe.
Kamfanin dillancin labarai na AP, ya ruwaito cewa, da bude kan iyakar ne, dumbin ‘yan Venezuela suka bazama cikin kasar ta Colombia, domin amfani da wannan dama su sayi kayayyakin da ba sa iya samu a kasars.
Venezuela ta jima cikin rikicin siyasa, lamarin da ya dakile samun ababan more rayuwa ya kuma jefa al'umar kasar cikin mawuyacin hali.
Tun a watan Fabrairu, Venezuela, wacce ke kudancin yankin Amurka, ta ba da umurnin rufe kan iyakokinta da yankunan Aruba, Bonaire, Curacor, Brazil da Colombia, a lokacin da ‘yan adawa suka yi yunkurin shigar da kayayyakin abinci da na magunguna zuwa cikin kasar ta Venezuela.