Shugaban kasar Venezuela da babban jami’in hukumar zabe jiya Laraba, suka musunta cewa an yi coge a adadin mutanen da suka fito kada kuria, da kara a kalla miliyan daya a zaben dake cike da tankiya da zai ba majalisa ikon sake rubuta kundin tsarin mulkin kasar.
Shugabar hukumar zaben ta kasa Tibisay Lucena tace irikirarin da wani kamfanin fasahar zabe na kasar Birtaniya yayi rashin sanin ya kamata ne, kuma tayi barazanar daukar matakin shari’a a kan kamfanin.
Lucena tace, wannan ra’ayi ne na kamfanin da rawar da ya taka kawai a zaben shine samar da tallafi ta fannin amfani da fasahar zamani da ba shi da wata alaka da sakamakon zaben.
Shugaban kamfanin Smartmatic na kasar Birtaniya, Antonio Mugica ya fada a birnin London jiya Laraba cewa, babu tantama, adadin kuri’un da aka sanar ba daidai bane. Sai dai bai bayyana ko murda kuri’un ya sauya sakamakon zaben da aka gudanar ranar Lahadi ba.
Shugaba Nicolas Maduro ya fada a jawabin da ya yi a tashar talabijin cewa, Amurka da Birtaniya ne suka matsawa Mugica lamba. Ya sake jaddada matsayin gwamnati cewa, mutane miliyan takwas suka kada kuri’a, ya kara da cewa ba domin masu zanga zanga sun toshe hanyoyi ba, da mutanen da suka kada kuri’a sun kai miliyan goma.