Hukumar tsaron kasar Uzbekistan ta ce an sami sake farfadowar ayyukan masu tsattsauran ra’ayin addini a kasar da ke tsakiyar Asiya, amma tarihin gwamnatin na fakewa da tsattsauran ra’ayin addini domin tunkarar ‘yan adawa ya sa masu lura da al’amura shakku akan lamarin.
WASHINGTON DC —
Hukumar Tsaron Kasar a ‘yan watannin nan ta sanar da ayuka da dama na yaki da masu tsattsauran ra’ayin addini ciki har da na 8 ga watan Satumba a babban birnin kasar Tashkent.
An tsare ‘yan Uzbek shida bisa zargin rarraba sakwannin telegram dake kira ga ‘yan kasar da su je Syria domin shiga wata kungiyar ‘yan ta’adda.
Uzbekistan na da yawan jama’a miliyan 33, inda kashi 94 cikin dari musulmi ne a cewar ma’aikatar harkokin wajen kasar. Sauran kashi 3.5 cikin dari kuma mabiya addinin gargajiyar Rasha ne.
Ragowar kusan kashi 3 cikin dari kuma sun hada da ‘yan katolika, Kiristoci ‘yan Koriya da sauran addinan gargajiya daban-daban.