Uwargidan Shugaban Najeriya Ta Kafa Kwamitin Yakin Neman Zabe

aisha buhari

Uwar gidan shugaban Najeriya Aisha Buhari ta kafa kwamitin yakin neman zaben maigidanta da jawo mutanen da a ka yi tsammanin za su samu manyan mukamai tun 2015 amma ba su samu ba; ta shigar da su kwamitin.

Mutanen da a ka ga sunan su a matsayin masu ba da shawara sun hada da Burgediya Janar Lawal Jafaru Isa da a ka yi tsammanin zai zama ministan tsaro ko mai ba da shawara kan harkar tsaro amma ba a ga hakan ba, kuma ya ci gaba da zama mai tafiyar shugaba Buharin ba tare da korafi ba.

Kazalika an ga sunan Hajiya Naja’atu Muhammed da ta taba kin karbar wani mukamin shugabar majalisar kula da jami’ar taraiya ta Dutse, kafin a ba ta memba a kwamitin hukumar ‘yan sanda.

Sai tsohon babban sufeton ‘yan sanda Sulaiman Abba wanda a ka tabbatar janye jami’an tsaro da hana tada tarzoma a dakin ba da sakamakon zabe na 2015; ya sanya tsohon shugaba Jonathan kwabe shi daga mukamin da nada tsohon sufeto Solomon Arase. Za a ce shi ma sai bayan shekaru 4 a ka ga sunan sa ya bullo a mai ba da shawarar kamfen.

Akwai kuma irin su Pauline Tallen da ta ki karbar matsayin jakada da baiyana cewa ba za ta so ficewa daga Najeriya ba don ta na kula da mijin ta da ba shi da lafiya. Tun farko an yi sa ran Mrs.Tallen za ta zama minista daga jihar Filato.

Aisha Buhari da Dolapo Osinbajo ne za su jagoranci kwamitin inda uwar gidan gwamnan Nassarawa Mairo Almakura za ta zama jami’ar kula da jihohin arewa yayin da Mrs.Adejoke Adefulure za ta zama mai kula da kudu.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu Elhikaya

Your browser doesn’t support HTML5

Aisha Buhari Ta Kafa Kwamitin zabe-4:00"