Uwargidan Shugaba Buhari Ta Kira Masana'antu Su Tallafawa Jihar Borno

Hajiya Aisha Buhari, uwargidan shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Yayinda ta kai ziyara jihar Borno uwargidan shugaba Buhari ta kira masana'antun Najeriya dake ciki da wajen jihar da su taimaka mata ganin irin mawuyacin halin da rikicin Boko Haram ya jefata ciki

Lokacin da uwargidan shugaba Buhari ta kai ziyara jihar Borno ta kira masana'antu da su tallafawa jihar Borno wadda rikicin Boko Haram ya daidaita al'ummarta tare da lalata muhallai masu dimbin yawa.

Hajiya Aisha Buhari tace jihar na bukatar taimakon gaggawa game da irn halin kakanikayi da al'ummar jihar suka samu kansu ciki saboda rigingimun da suka addabesu sanadiyar ta'adancin Boko Haram.

Uwargidan shugaba Buhari ta mikawa jihar kayan tallafi da ta zo dasu. Kayan sun hada da abinci da tufafi da wasu na masarufi da ma kayan bukatu irin na yau da kullum. Tace abubuwa da ta kawo soma tabi ne kawai saboda zata kawo wasu kayan masu yawa.

Hajiya Aisha Buhari ta kuma kafa wani kwamiti mai mutane 11 a karkashin jagorancin matar gwamnan jihar Borno Hajiya Nana Kashim Shettima kana ta dorawa kwamitin alhakin raba kayan da ta kawo da ma wadanda zata aika masu.

A cikin jawabinta Hajiya Aisha tace yaki da Boko Haram ya zo karshe. Wadanda suka rasa rayukansu sanadiyar rikicin Allah ya yi masu gafara. Wadanda kuma suka rasa abun duniya Allah ya mayar masu.

Takira duk wadanda suke da kayan taimako su ba mutanen Borno domin a taimaka masu.

Matar gwamnan Borno Nana Shettima tayi godiya da taimakon da matar shugaban kasa ta kawo tare da yin alkawarin cewa abubuwan da aka kawo zasu kai hannun wadanda suka cancanta su samu.

Gwamnan jihar Ibrahim Shettima ya yabawa Hajiya Buhari game da namujin kokarin da tayi na taimakawa jihar.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Uwargidan Shugaba Buhari Ta Kira Masana'antu Su Tallafawa Jihar Borno - 3' 55"