Uwargidan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta APC, Hajiya A’ishatu Buhari, ta musanta rade-radin da ake yi na cewa an jefe su a garin Ilori da ke jihar kwara.
Yayin da ya ke magana a madadin uwargidan Buharin, dan’uwan ta Mahmud Halilu Ciroma, ya ce babu wani abu makamancin haka da ya faru, ya na mai cewa labara ne da aka kago shi.
A yau ne wasu jaridun Najeriya suka ruwaito cewa an jefi uwargidan Buharin tare da matar dan takarar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.
To sai dai dan uwan uwargidan dan takarar shugaban kasa, ya ce su ma a jaridu su ka labarin.
“Wanna batu kamar yadda kuka ji muma haka muka ji, wannan abu kwata-kwata bai faru ba, yadda suka taso daga filin jirgi aka tare su suka wuce gidan gwamnati, suka je gaisuwan ban girma a gidan mai martaba sarki Ilorin, daga nan ne aka ce an yi jifan, kuma ba a yi jifa ba, babu wanda aka jefa.” In ji Mahmud.
Muryar Amurka ta kuma tambaye shi, yadda aka yi wasu jaridun Najeriya suka ce har an fasa motoci guda goma yayin da ya ke musanta lamarin, sai ya ce:
"Muma abin ya bamu mamaki domin a tawagar babu wanda ya ga wani wanda ya yi jifa."
Your browser doesn’t support HTML5