Amurka za ta Sayar wa Saudiyya Makaman Dala Biliyan 60

  • Ibrahim Garba

A wannan hoton da aka ran Lahadi, 25 ga Janairun 2009, Jiragen yaki samfurin F-15 ne mallakin Sa'udi Arabiya ke shawagi

Amurka ta amince ta sayar wa Sa’udi Arabiya jiragen yaki safurin jet, da masu saukar ungulu na kai farmaki da dai sauransu a kan kudi dala biliyan 60.

Amurka ta ce za ta yi ciniki mafi girma a tarihin sayar da makamanta, inda ta amince ta sayar wa Sa’udi Arabiya jiragen yaki samfurin jet, da masu saukar ungulu na kai farmaki da dai sauransu a kan kudi dala biliyan 60.

Wani jami’in Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Andrew Shapiro ya fadi yau Laraba cewa za a gudanar da wannan harkar ce daga yanzu zuwa shekaru 15 ko 20. Wannan harkar na nuna cewa Amurka za ta sayar wa kawarta ta Gabas ta Tsakiya sabbin jiragen yaki sanfurin jet guda 84 da kuma tsoffin da aka yi masu kwaskwarima guda 70.

Wannan harkar ta kuma hada da sayar da jiragen yaki masu saukar ungulu guda 178 da su ka hada da samfurin Apache da Blackhawks da Little Birds da kuma makamai masu linzami masu inganci, da na’urar hangen jirage ta radar da sauran kayan soji.

Shapiro ya ce wannan cinikin ya dace da “fadadaddun muradan tsaron” Amurka a yankin Tekun Fasha. Ya kuma ce hakan zai taimaka wajen samar wa Sa’udi Arabiya “halattattun bukatunta na tsaro.”

Masu nazarin al’amura sun ce sayar da wadannan makaman za ta kasance wani martani ga karfin sojin Iran da ke ta karuwa. Manyan kasashen Turai za zargin Iran da yinkurin shirin makamin nukiliya, to amman Iran ta ce shirin makamin nukiliyarta na zaman lafiya ne.