Jiya Asabar an yi wa wata wakiliyar majalisar dokokin Amurka mummunar rauni,bayan wani harbi da aka yi cikin yankin mazabarta dake kudu maso yamacin jihar Arizona,har aka kashe mutane shida ciki har da wani alkalin kotun tarayya,da wata yarinya ‘yar shekara tara.
‘Yar jam’iyyar Democrat,an harbi Gabrielle Gifford ne a akai, tana daga cikin mutane 19 da aka harba a harabar wani babban kanti dake birnin Tucson.
Shugaba Brack Obama wanda ya yi magana a yammacin jiya Asabar daga Fadar White House, ya kira harbin wani "mummunar al’amari" daga nan yace darektan hukumar binciken manyan laifuffuka na Amurka(FBI) yana kan hanyar zuwa Arizona domin ya jagoranci bincike kan wan nan lamari.
Darektan Asibiti da aka kai wakiliyar ya yace yana da kwarin guiwa zata warke.
‘Yar shekara 40 da haifuwa, Gifford tana wani taro ne da mazauna mazabarta.'Yansanda suka ce wadanda ke kusa sun yi kokuwa har suka rinjayi dan bindigan,wanda aka ce sunansa Jared Loughner, dan shekara 22 da haifuwa.