Shugaban Amurka Barack Obama Ya kira Taro Da Shugabannin Republican Da na Deocrat Domin Duba hanyoyinda Zasu Yi Aiki Tare

Shugaban Amurka Barack Obama ne yake tsokaci ga manema labarai,bayan ya gana da manyan jami'ai d a minsitocin gwamnatinsa, afadar White House ranar Alhamis

Sakamakon nasara da jam'iyyar Republican ta samu a zaben 'yan majalisa da ake yi ako wani lokacin rabin wa'adi na sabon shugaban kasar Amurka,ganin yanzu Jam'iyyar Republican ta samu rinjaye a majalisar wakilai ta tarayya.

Shugaban Amurka Barack Obama, ya gayyaci shugabannin Jam’iyyar Republican da Democrat domin su yi shawarwari kan hanyoyi da za su yi aiki tare, bayan jam’iyyar Republican ta sami rinjaye a majalisar wakilai a zaben shiga majalisa da ake yi a dai dai tsakiyar rabin wa’adin sabon shugaban kasar Amurka.

Da yake magana bayan taron majalisar ministocinsa Alhamis din nan,Mr. Obama yace ya yi magana da shugaban marasa rinjayeMitch McConnell da wakili John Boehner, tare da shugaban masu rinjaye Harry Reid, da kakakin majalisa Nancy Pelosi, su zo fadar White House domin shawarwari ranar 18 ga watan Nuwamba.

Ana sa ran wakili John Boehner ne zai zama sabon kakakin Majalisar dokokin Amurka,cikin watan Janairu lokacin sabuwar majalisar zata fara aiki.