Amurka Da Turai Sun Yi Tir Da Hukuncin Da Wata Kotu a Rasha Ta Zartas Wa Khodorkovsky

  • Ibrahim Garba

Mikhail Khodorkovsky bayan da aka zartas masa da hukunci a wata kotu a birnin Moscow

Gwamnatocin Yammacin Duniya sun yi tir da tsattsauran hukuncin daurin da wata kotu a birnin Moscow ta zartas ma hamshakin mai kamfanin man fetur dinnan Mikhail Khodorkovsky

Gwamnatocin Yammacin Duniya sun yi tir da tsattsauran hukuncin daurin da wata kotu a birnin Moscow ta zartas ma hamshakin mai kamfanin man fetur dinnan Mikhail Khodorkovsky, wanda wasu ke ganin shari’ar da aka masa wata alama ce ta gazawar ka’idar shari’a a Rasha.

Khodorkovsky da abokin huldar kasuwancinsa Platon Levedev sun sami karin shekaru 14 a gidan yari, wanda ya kawo karshen shari’ar da aka yi watanni 20 ana yi, wadda ta kuma kara shekaru shida kan guda takwas din, wanda har sun shafe biyu daga ciki a tsare.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Mark Toner, ya fadi jiya Alhamis cewa wannan hukuncin ya yi kama da amfani da tsarin shari’a don cimma wata manufar da ba ta bisa ka’ida.

Lauyan da ke kare wadanda ake zargin, Yuri Shmidt ya ce an yake hukuncin ne haka, saboda matsin lambar Firayim Ministan Rasha Vladimir Putin. A ta bakinsa, “ Yau Putin ya nuna wa Kotu alamar ko waye ke da iko.”

Alkali Viktor Danilkin jiya Alhamis ya zartas wa Khodorkovsky da hukunci mafi tsanani kamar yadda masu gabatar da kara su ka nema bayan an same shi da laifin wawurar kudin kamfaninsa, Yukos.

Uwar Khodorkovsky, Marina, jiya Alhamis ta bayyana hukuncin da cewa shirme ne kawai.

Khodorkovsky, wanda ada shi ne mafi arziki a Rasha, arzikin nasa ya tabu bayan day a kalubalanci Vladamir Putin a lokacin ya na Shugaban kasa ta wajen mara baya ga abokan hamayyarsa.

Shugabar Jamus Angela Merkel ta fadi jiya Alhamis a cikin wani jawabi cewa manufofin siyasa sun shafi shari’ar.