Wannan musanya ita ce ta farko cikin watanni, kuma ta kunshi musanyar fursunoni kusan 400 a tsakanin sassan guda biyu
WASHINGTON D.C —
Hukumomin Ukraine da ‘yan tawayen dake samun goyon bayan Rasha sun fara musayar fursunoni a yankin gabashin Ukraine yau Laraba.
Wannan shine karon farko da aka yi babbar musanyar tun bayan watanni da suka gabata, kuma ita ce ta fi yawa tun daga lokacin ballewar rikicin ‘yan awaren Rasha a wannan yankin na Soviet a shekarar 2014.
Yarjejeniyar ta bukaci Ukraine ta mika fursunoni 306 ga ‘yan tawaye ita kuma ta karbi musayar fursunoni 74.
Rikicin na gabashin Ukraine ya balle ne a watan Afirilun shekarar 2014 bayan da Rasha ta mamaye yankin Crimea wata daya kafin a fara rikicin.