Sojoji sun shafe awa biyu da rabi sun a binciken gidansa kafin su kama shi.
Wannan yana zuwa ne a yayin da kasar Uganda take shirin gudanar da zaben shugaban kasa ranar 18 ga wannan wata, inda shugaba Museveni, wanda yah au mulki tun shekarar 1986, yake neman a sake zabensa.
Kakakin gwamnatin Uganda, Ofwono Opondo, yace an kama Janar Sejusa a saboda yana tsoma hannunsa a cikin harkokin siyasa.
Opondo yace Janar Sejusa yana jawabai a bainar jama’a yana barazanar harhada kawunan jama’a su kauracewa zaben wanda a cewarsa na bagu ne kawai.
Lauyan Sejusa, Ladislaus Rwakafuzi, ya fadawa VOA cewa kama janar din da aka yi haramun ne a saboda sojoji basu da takardar iznin kama shi, kuma sun ki bayanin dalilansu na yin hakan.
Lauyan yace watakila kama Janar din yana da alaka da zabe mai zuwa a saboda yana bayarda shawara ga babban shugaban adawa na kasar, Kizza Besigye, kan yadda za a iya hana magudi a lokacin zabe.