Uganda, Botswana da Ghana Sun Fi Yawan Mata 'Yan Kasuwa

Wasu matan Afurka a kasuwa

Uganda, Botswana da Ghana su ne kasashe uku na farko a duniya wajen yawan mata 'yan kasuwa da masu sana'o'i.

Kasar Botswana ce ke kan gaba, sai Uganda sannan Ghana, a matsayin kasashen da suka fi yawan mata masu kasuwanci a duniya.

Binciken da cibiyar kula da cigaban mata 'yan kasuwa ta gudanar ta 2021, wato 2021 Mastercard Index of Women Entrepreneurs (MIWE), ya nuna cewa mata 'yan kasuwa a Afirka suna da juriya da sanin yanayin kasuwanci wanda a shekara uku jere, kasar Botswana ta samu kaso (38.5%), Uganda (38.4%) Ghana (37.2%) wadanda suke matsayin kasashen a afrika da ke da mafi yawan mata masu kasuwanci a duniya.

Wannan binciken shi ne karo na biyar da cibiyar kula da cigaban mata 'yan kasuwa, wato MIWE, ta gudanar.

Duk da kalubalen da annobar cutar Covid-19 ta haifar da koma bayan tattalin arziki da ake fuskanta a duniya, binciken da cibiyar ta Mastercard ta yi ya nuna cewa mata masu sana'ar kansu a Afirka suna da juriya da sanin yanayin kasuwanci musamman masu karamin karfi da matsakaitan tattalin arziki, galibi sun zarce maza ta fuskar harkokin kasuwanci.


Rahoton har iyalau ya nuna cewa kasashen Najeriya, Angola da Ghana sun kasance a matsayi na farko a duniya wajen hada hadar mata 'yan kasuwa a matakin kasa da kasa.

Ebehigie Momoh, Manaja kuma Shugaban Kula da Harkokin Kasuwancin Yankin Yammacin Afirka a cibiyar ta MasterCard, ya taya kasashen Afirka murna saboda kokarinsu na kasuwanci da kuma matakin karfafa kananan sana’o’i.

Ya kara da cewa “mata a kasashen Botswana, Uganda, Ghana, Najeriya da Angola sun yi fice, idan za a kwatanta mata masu jajircewa wajen ciyar da kansu da iyalansu, duk da kalubalen kudi da fannin fasaha da suke fuskanta. A cikin wannan yanayin tattalin arzikin, mata suna iya yin amfani da damarmaki don zama masu Sana’ar kansu, shugabanni da kwararrun ma'aikata ko masu fasaha.

Malama Hasana, shahararriyar 'yar kasuwa a Ghana, ta ce kasuwanci ya ba mata daraja da martaba. kasuwanci ya sa mata suna kare mutuncinsu. Ta ce nan gaba mata za su zama mafiya tafiyar da kasuwanci a duniya.

Ya na daga cikin dabarun da cibiyar kula da cigaban mata ta mastercard ta bullo da shi do a gane cewa an harzuka mata shiga samar da sana'o'in kansu da kansu. Cibiyar ta sha alwashin hada mata miliyan 25 a sassan duniya domin dada tayar da komadarsu ta fuskar amfani da nau'rar zamani wajen kasuwanci.

Saurari cikakken rahoton Hauwa Abdulkarim:

Your browser doesn’t support HTML5

07-20-22 Tayar Da Komadar Mata.mp3