Hukumar dake kula da wasan kwallon Kafa ta nahiyar Turai (UEFA) ta tunasar da alkalan wasa batun kare mutuncin ‘yan wasa da kuma daukar kwakwaran mataki wajan hukunta dan wasan da ya nemi raunata dan uwansan dan wasa walau da gangan ko kuma rashin sani.
UEFA ta fadi hakan ne sakamakon korafin da mai horas da kungiyar Manchester city Pep Gaudiola yayi kan raunin da akaji wa dan wasansa Leyro Sane a wasan su da Cardiff City na gasar cin kofin kalu bale na kasar Ingila. FA Cup.
Shugaban hukumar ta UEFA Alexsander Ceferin, ya shaidawa shugaban alkalan wasannin kwallon Kafa Pierluigi Collina. cewa muna son muga ‘yan wasa suna wasa don haka ya kamata alkalan wasa suyi aikinsu karmar yada yakamata domin gujewa yanayin da zai sanya wa wani dan wasan cikin shakka saboda mummunan rauni wanda kalubalene ga dan wasa.
Haka kuma "Dole ne ‘yan wasan su fahimci cewa ya kamata su girmama abokanan wasan su kuma su duba ciwar irin haka in ta faru dasu Yaya zasuji kansu.
A yau Talata za'a dawo fafatawa a gasar ta cin kofin zakarun turai (UEFA Champions league) zagaye na sha shida, inda Juventus zata kara da Tottenham sai kuma Basel ta karbi bakuncin Manchester City da misalin karfe tara saura kwata na dare agogon Najeriya Nijar Kamaru da kasar Chadi.
Your browser doesn’t support HTML5