Hukumar dake kula da wasan kwallon kafa ta nahiyar turai, (Uefa) ta fidda sunayen ‘yan wasa guda ukku da za'a zabi daya daga cikinsu wanda zai lashe lambar yabo ta gwarzon shekara, a fagen kwallon kafa bangaren maza a nahiyar turai.
Cikin jerin sunayen akwai shahararrun ‘yan wasan kwallon na duniya, kamar haka,
Lionel Messi, dan kasar Argentina, mai taka leda a kungiyar Barcelona, sai Cristiano Ronaldo, na Real Madrid, dan kasar Portugal, da kuma mai tsaron raga na Juventus, Gianluigi Buffon.
Dukkan ‘yan wasan sun taka rawar gani a bangaren tamola a nahiyar turai a shekarar da ta gabata, 2016/17.
Ita dai wannan kyauta ana mata lakabi da Gwarzon dan wasa na Turai ( Europe Best Player of The Year) a na bada ita ne, ga dan wasan da yafi taka rawar gani a nahiyar Turai, walau a kungiyarsa, ko kwallon kafa ta kasarsa ta nahiyar Turai, ko kuma kulob dinsa.
A shekarar da ta gabata dai dan wasan gaba na Real Madrid Cristiano Ronaldo, ya lashe kyautar, kuma ya samu nasarar karbar wannan kyautar har sau biyu.
Sai takwaransa Lionel Messi, na Barcelona, shi ma ya samu nasarar lashe kyautar sau biyu.
A cikin jerin sunayen ‘yan wasan da suka taba samun nasarar lashe wannan kyautar kuwa sun hada da Andres Iniesta, da Franck Ribery, wasu masu horas da kungiyoyin kwallon kafa na nahiyar Turai su Tamanin da kuma wasu zababbun ‘yan jaridu guda hamsinne suka jefa kuri'arsu wajan fidda wadannan sunayen, inda Luka Modric, ya zo na hudu a jerin sunayen sai Toni Kross, da kuma Paulo Dybala, na juventus.
A ranar 24 ga watan Ogusta 2017 za'a bayyana sunan wanda ya samu nasarar zama gwarzon dan wasan na turai.
Your browser doesn’t support HTML5