Kamfanin sadarwar yanar gizo na Twitter ya sanar da cewar ya kammala shirin sa tsaf, don fito da wata manhaja da zata dinga taimakawa mutane wajen zaban labaran da suke da sha’awa akai.
Sabon tsarin mai suna “Topics” zai fara aiki daga ranar 13 ga watan Nuwambar wannan shekarar. Haka kuma duk mutane masu amfani da wayar hannu ta android da apple, zasu iya samun sabon tsarin daga ranar a shafukansu.
Kamfanin ya kara da cewar, zamu fara wannan shirin ne da labarai masu daukar hankali, kamar wasannin kwallo, a cikin ‘yan makonni kuwa sai a kara inganta shi da sauran labarai masu kayatarwa.
Tun dai a farkon wannan shekarar ne kamfanin na Twitter, ya sanar da cewar zai samar da wasu hanyoyi ga ma’abota shafin, wajen zabar labarai da suka shafi kananan sana’o’i don bibiya.
Mutane zasu iya amfani da kafar wajen aika sakon gaggawa.