Twitter Da Facebook Ba Zasu Halarci Taron White House Ba

Babu cikakken bayani akan babban taron da za a yi a White House, da kuma wadanda aka gayyata, amma dai taron na zuwa ne a dai-dai lokacin da a ke caccakar kamfanonin a bangarori daban-daban.

Manyan masu ra’ayin ‘yan mazan jiya, na shirin zuwa fadar shugaban Amurka ta White House, yau Alhamis don tattaunawa akan yadda za a tunkari batun rahotanni da labaran dake fitowa daga kafafen sada zumuntar yanar gizo.

Amma manyan kamfanonin sada zumunci na Twitter da Facebook ba za su je taron ba, rahotannin sun bayyana cewa ba a gayyace su ba.

Wasu na nuna cewa kamfanonin na sada zumunta na danne ra’ayoyin masu ra’ayin mazan jiya. Wasu kuma suna cewa, kamfanonin ba sa kare ma’abota shafukan daga labaran da ba na gaskiya ba, da kuma rubuce-rubucen batanci yadda ya kamata.