An yi kira ga wadanda abin ya shafa a Najeriya da su tabbatar cewa ana zaban mutanen kirki a matsayin shugabanni a matakai daban-daban, a maimakon kawai su rinka shirya tarurrukan tunawa da mutanen kirki da su ka gabata.
Masanin ilimin zamantakewa Furfesa Usman Bugaje ya lura cewa a siyasar Najeriya ba a barin mutane na gari su shugabanci jama’a sai dai wadanda su ke da kudi koda kuwa ba ta hanyoyin halas su ka samo kudaden ba. Muddun sai wadanda su ka iya yaudara da kuma wadanda su ka arzuta kansu da kudaden jama’a ake bari su shugabanci jama’a a Najeriya to babu inda za a je.
Ya ce an san mutanen kirki a kowace unguwa a Najeriya; don haka da ganga ake zaban baragurbi sannan daga baya kuma a zo ana kuka.
Furfesa Bugaje ya yi takaicin yadda yara kanana ke gararanba a tituna da sunan almajiranci. Ya ce babu wata kasar da ta san ciwon kanta da za ta bar yara kanana irin haka su yi ta kai-komo ba abinci kuma babu ilimi. Ya ce irin haka shi ke kawo rashin kwanciyar hankali da cigaba a kasa.
Ga dai wakilinmu Isah Lawal Ikara da cikakkiyar hirar:
Your browser doesn’t support HTML5