Rundunar Sojin Turkiyya ta ce ta yi asara mafi muni ta rayukan sojojinta a rana guda, a farmakin da ta ke kai wa kan ‘yan bindiga a arewacin Siriya.
Sojojinta akalla 7 su ka mutu jiya Asabar.
Biyar daga cikinsu sun mutu ne a yankin Afrin, lokacin da aka kai hari kan tankar yakin da su ke ciki.
Biyu kuma sun mutu ne tun da farko a jiya din - daya daura da inda aka kai hari kan tankar yakin, dayan kuma daura da kan iyakar Siriya da Turkiyya.
A martanin da ta mayar, Turkiyya ta ce ta jiragen yakinta sun kai hari kan wasu wurare na Turkiyya da ke yankin da aka kai hari kan tankar yakin.
Tun a karshen watan jiya ne Turkiyya ta fara kaddamar da farmaki kan dakarun Kurdawan YPG da ke Siriya, wadanda Turkiyya ke daukawa a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda masu alaka da Kungiyar awaren Kurdawa da ke Turkiyya. Zuwa yanzu dai Turkiyya ta rasa sojoji 14 a wannan fadan.