Turkiyya Ta Kakkabo Jiragen Syria

Yadda sojojin Turkiyya ke kai hari cikin Syria

Kafar yada labaran gwamnatin Syria SANA, ta sanar jiya cewa sojojin Turkiyya sun kai hari kan jiragen saman kasar a Lardin Idlib.

SANA ta ba da rahotan cewa matukan jirgin sun fice daga jirgin, sun kuma sauka lafiya ba tare da jin rauni ba inda suka yi amfani da lemar sauka.

Kungiyar sa ido akan harkokin ‘yancin dan Adam a Syria mai hedkwata a Burtaniya ta ce jiragen biyu sun fado a wani yankin kasa da ke karkashin iko gwamnati, jim kadan da harbo su da jiragen yakin Turkiyan samfirin F- 16 suka yi.

Ma’aikatar tsaron Turkiyya ta fadi cewa an harbo jiragen ne bayan da aka kakkabo daya daga cikin jiragenta marasa matuka.