A Turkiyya, hukumomin kasar sun ce sun kusa gano ko ayyana ko wannene mutumin da ake zargin da kai hari a shigar sabuwar shekara a wani klub a birnjn Istanbul, ya halaka mutane 39, galibinsu 'yan kasashen wajekuma Kungiyar ISIS ta dauki alhakin kai harin.
WASHINGTON DC —
Mukaddashin Firayim Minista kasar Numan Kurtulmus, ya gayawa manema labarai jiya Litinin cewa, hukumomi sun samu alamun halitta da hoton yatsu da kuma kamannin maharin. An rarraba hoton maharin da kemarorin tsaro suka dauka kodashike bashi da haske ainun a duka kafofin yada labarai a sassan kasar duka. Haka nan Mr. Kurtulmus ya tabbatada an kama akalla muane takwas dangane da harin.
An fara harin ne daf da tsakiyar dare agogon kasar, lokacinda maharin ya kashe wani dansanda da wani farar hula daya a kofar shiga klub din, kamin daga bisani ya shiga wurin inda mutane kusan 600 galibinsu 'yan kasashen waje suke ciki.