Biyo bayan wani mugun hari da aka kai Suruc ranar Litinin hukumomin Turkiya sun rufe hanayar sadarwa ta twitter domin dakile yada labarin hallaka rayuka da aka yi.
WASHINGTON DC —
A Turkiya, hukumomin sun ce sun datse hanyar sadarwa zamani ta Twitter domin hana yada hotunan harin da aka kai a ranar Litinin a Suruc, inda akalla mutane 31 suka rasa rayukansu.
Jami’an kasar sun ce da zaran an cire hotunan a shafukan internet, za a maido da hanyar sadarwar ta Twitter.
Ya zuwa yanzu babu wanda ya dauki alhaki harin kunar bakin waken, ko da yake jami’an Turkiya sun yi amannar cewa mayakan ISIS ne suka kai shi.
Harin dai ya kaikaici wata kungiyar masu fafatuka ce, wadda mafi yawancin mambobinta dalibai ne da ke shirin zuwa birnin Kobani da ke Syria domin a sake gina garin, wanda ke iyaka da kasar ta Turkiya.