Turereniyar da aka yi akan wata Gadar jirgin kasa a babbar cibiyar Kasuwancin Indiya yayi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane 22 yayin da wasu fiye da 20 suka ji raunuka a sanyin safiyar Jumma’a.
Jami’I mai magana da yawun ma’aikatar Jiragen kasan yayi gargadin sai ta yiwu a sami karin wadanda fitinar ta rutsa da su.
Mutane masu yawa ne suka nemi mafaka a gadar a Elphinestone dake tsakiyar birnin, yayin da ake ruwan sama kamar da bakin kwarya ya barke babu zato ba tsammani.
Ya zuwa yanzu dai babu tabbacin abinda ya jawo turmutsitsin, duk da dai akwai rahotanni da suke nuni da cewa akwai jita-jitar da take bazuwa cewa gadar ce zata karye bayan da wani baraguzan kankare ya fado wanda ya sa mutane suka fara turereniyar barin Gadar.
Gadar dai itace ta hada tashar Elphinestone da kuma tashar Parel da ke yammacin Birnin a Kudancin India.
Mafiya yawan lokaci akwai turmutsi a awannin safiya, sakamakon fasinjoji na amfani da hanyar wajen fita daga Jirgi a tashar Jirgin kasa da ke kusa da wurin.