Tunawa Da Umar Abdul'aziz Wudil - Fadar Bege

Marigayi Umar Abdul'aziz Wudil, wanda aka fi sani da sunan Fadar Bege

Filin "A Bari Ya Huce" na ranar asabar zai gabatar da bayani daga bakin Sayyadi Sharif Sani Janbulo da kuma wakokin bege na Fadar Bege
Jama'a daga sassa dabam-dabam na duniya sun ci gaba da bayyana jajensu game da rasuwar shahararren mai wakar bege, Umar Abdul'aziz, wanda aka fi sani da sunan Fadar Bege, daya daga cikin mutanen da suka fi fita a wakokin addinin Islama da ake kira wakokin Begen Manzon Allah.

Filin "A Bari Ya Huce" ya tattauna da mutumin da ya rike Fadar Bege, ya koyar da shi yake kuma koyar da shi har zuwa rasuwarsa, Sayyadi Sharif Sani Janbulo, wanda kuma yake zama kamar mahaifi ga shi marigayin.

Sayyadi Sharif Sani ya tabo batun rayuwar Umar Abdul'aziz, da yadda ya sha wahala a lokacin da yake tashi, da yadda ya fara wakokin bege, da yadda ya koma wurinsa da zama a Kano, har zuwa rashin lafiya da kuma rasuwarsa.

Haka nan shi ma babban aminin Fadar Bege, Muhammad Hafiz Abdallah, yayi magana kan yadda marigayin ya rasu a hannunsa, da kuma abubuwan mamakin da yayi ta gani a lokacin rasuwar marigayin da kuma bayan nan.

A kasance tare da filin "A Bari Ya Huce" ranar asabar da karfe 6 na safiya agogon Najeriya.

Ga somin tabin hira da Sayyadi Sharif Sani Janbulo kan marigayin.

Your browser doesn’t support HTML5

Tuna Fadar Bege - Kadan Daga Bayanin Sayyadi Sharif Sani - 3:19