Tunanin Zuci Na Sarrafa Kwamfuta Mai Kwakwalwa

Kamar almara, amma akwai wasu na’urorin fasahar zamani da ake sanyawa dake ba masu amfani da su damar sarrafa kwamfuta da tunaninsu. Wasu kwararru a fannin fasaha dake Anguwar Brooklyn a jihar New York, sun kirkiro wata na’ura da ake makalawa a kai don sarrafa kwamfuta.

Ita dai wannan na’urar da ake kira Notion wadda kamfanin Neurosity ya fito da ita, wadda kuma ake saidawa dala $900, ta na nazarin yanayin kwakwalwar bil’adama, ta kuma yi amfani da tunanin mutum don aiwatar da wasu abubuwa. Ma’ana, na’urar na sarrafa kwamfuta bisa ga tunanin wanda ya makala ta.

Hakan na kuma nufin mutum ba ya bukatar na’urar Mouse ta jikin kwamfuta don cimma buri.

Sai dai ita wannan na’urar na bukatar maida hankali, a saboda haka Notion na bayyanawa mai amfani da ita makin yanayin maida hankalinsa.