Tun Makon Jiya Gwamnatin Kano Ta Soma Bikin Cika Shekaru 50 da Kafa Jihar

Dr. Abdullahi Umar Ganduje gwamnan Kano

Tun makon jiya ne aka fara jerin taruka da laccoci domin murnar bikin cika shekaru hamsin da aka kirkiro jihar Kano, jihar da tafi kowace jiha yawan jama'a a Najeriya

Bukukuwan da ake yi sun hada da dandalin bitar nasarori da jihar ta samu da kuma kalubalen da ta fuskanta ko kuma take fuskanta.

Tuni masana tarihi da 'yan siyasa da masu tsokaci kan alamuran yau da kullum suka fara bayyana mabanbancin ra'ayi dangane da cewa ko jihar ta samu cigaban da aka yi tsammani cikin wadannan shekaru hamsin ko kuma a'a.

Alhaji Abu Muhammad Fatakima tsohon shugaban jam'iyyar PRP a jamhuriya ta biyu na cewa gwamnan farko na jihar Alhaji Audu Bako duk da cewa yayi mulki lokacin yaki har tsawon shekara tara yayi kokarin dora jihar kan godaben cigaba. Yace an yi sa'ar samun irinsa a lokacin. Da duk gwamnonin da suka biyo bayansa sun bi sahunsa da yanzu Kano ba haka take ba. Yace wasu sun kauce hanyar da ya dora jihar amma wasu kuma sun kamanta.

Inji Alhaji Abu Muhammad daga cikin wadanda suka kamanta Alhaji Abubakar Rimi yana ciki. Yayi gwargwadon ikonsa. Bayansa rashin kishin kasa ya haddasar da hasarar shekarun da suka shude.

Galibin wadanda suka bada kasida sun amince Kano ta bunkasa a shekarun baya musamman ta fuskar masana'antu, kasuwanci da ayyukan noma ga kuma fannin ilimin arabiya da na zamani. Sai dai a baya bayan nan an samu koma baya idan ma aka yi la'akari da yawan masana'antun dake rufe a Kano yanzu. An kuma samu koma baya a wasu bangarori daban daban.

Malam Bashir Muhammad Bashir wani kwararren dan jarida kuma mai sharhi kan alamuran yau da kullum na cewa wasu shugabannin basu da kishin kasa. Idan mutumin da ya karbi mulki baya son wanda ya gada duk wani aiki nagari da wanda ya gada ya soma sai ya dakatar dashi ya soma nashi. Yace a kasashen da suka cigaba kuwa ba haka lamarin yake ba. Duk aikin da zai taimaki kasa kowa ya karbi mulki a kasashen da suka cigaba ba zai daina ba. Yace yakamata idan ana son a cigaba a daina zubar da akidun baya masu kyau saboda banbancin siyasa.

Daraktan labaru na gwamnan Kano Salihu Tanko Yakasai yace gwamnantin Ganduje na hobasa wajen kammala ayyukan da ta gada daga magabatanta. Yace gwamnan ya yadda duk abubuwan da shekaru da shekaru an barsu basa aiki zai gyara domin su dawo su yiwa jihar aiki.

Ga rahoton Mahmud Irahim Kwari da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Tun Makon Jiya Gwamnatin Kano Ta Soma Bikin Cika Shekaru 50 da Kafa Jihar - 3' 27"