A daidai lokacin da manoma ke dab da cin moriyar nomansu a Najeriya, manoman yankin jihar Sokoto sun soma kokawa akan barazanar da tsuntsaye suka soma yi musu, abinda ka iya kawo cikas ga amfanin gona da ake tunanin samu.
Barazanar tsuntsayen masu jan baki a yankin jihar Sokoto na zaman tamkar murna ta koma ciki, duba da cewa an ga alamun samun kakar abinci mai kyau a wannan shekara ta 2020.
Akan dole, wasu manoman yankin suka rungumi wata dabara ta gargajiya ta korar tsuntsayen kamar yadda wani matashi mai suna Faruk daga yankin Dange Shuni ya bayyana.
Sambo Abubakar, daya daga cikin manoman yankin, ya ce tsuntsayen yanzu haka suna addabar dukan shuke-shuken da suka fara kosawa a gonaki.
Shugaban kungiyar manoma ta Najeriya reshen jihar Sokoto, Murtala Gagado Minannata, ya ce yanzu haka a kashi biyu bisa uku na jihar Sokoto ana fama da wannan matsalar. Ya kuma ce yanzu suna jira ne su ji halin da yankunan kananan hukumomi a jihar ke ciki don su hada rahoton da za su aika wa ma’aikatar gona ta jiha da tarayya don daukar matakin da za a taimaka wa manoma.
Jami'in ma'aikatar gona ta tarayya mai kula da sashen maganin tsuntsaye da kwari, Ya'u Makeri Kagara, ya ce ba a wuce wata daya da kammala feshin maganin kashe tsuntsaye a yankin na Sokoto ba. Ya kara da cewa tsuntsayen na shigowa ne daga jamhuriyar Nijer da kasar Benin, kuma harkar kasa da kasa dole sai da wata yarjejeniya kafin a hada kai a magance matsalar.
A watan Yuni ne gwamnatin tarayya ta kaddamar da aikin feshin kashe tsuntsaye a jihohin arewacin Najeriya guda 12 wadanda ke makwabtaka da kasashen waje wadanda ta nan ne tsuntsayen ke shigowa Najeriya.
Sai dai sake samun wannan matsalar na iya mayar da hannun agogo baya ga ci gaban da ake ganin ana samu a fannin noma wanda gwamnatoci ke ikirarin cewa suna ba shi kulawa ta musamman.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir.
Your browser doesn’t support HTML5