Wakiliyar Muryar Amurka Madina Dauda ta tambayi Sanata Ali Indume ko yana ganin wanda ya kada shi zabe zai koma jamiyyar su ta APC domin tafiyar tayi masa sauki?, sai ya amsa da cewa.
‘’A to ban sani ba zai iya yiyuwa tunda mutum ya damu ya tsaya wannan din wannan ma zai iya yiyuwa, amma ni wannan din naje munyi takara mun samu majilisar dattawa ni na nemi mataimaki na fadi na hankura yin ALLAH ne kuma shi yasa muke cewa yan uwan mu a can bangaren da basu samu ba suma shiga cikin zaben ba tunda abu ya riga ya wuce mu tashi mu kakkabe abinda muke ji dashi mu dawo musa hankalin mu a abinda zai taimaki yan Nigeria talakkawa suna nan suna jira sun gaji sun sha wuya a hannun gwamnatin PDP shekara 16 to kuma yanzu ba zai yiyu ace jamiyyar da muke cewa canji-canji kuma talakawa suna fata su fara ganin canji din azo ace majilisa suna cece kuce akan matsayi ba, matsayin nan ALLAH ya riga ya baiwa wanda zai baiwa mu kawai muci gaba da aiki, kuma alhamdullillahi haka din da ya faru tunda wuri yafi domin idan an fara da takaddama da gardama haka din tafiyar ina fatar zaiyi kyau nagaba’’.
Kasan kai kanka ka nuna tantama akan yadda APC da PDP zasu yi tafiya tare domin kowanne yana da raayi da manufofin jamiyyar sa da kuma raayin sa zaiyi wuya ace manufofin APC dana PDP suzo daya, gashi shi wancan dan majilisar dattawa dan PDP ne nayi maka wannan tambayar ce ganin cewa kana like minds kuma kokarin janyo unity forum dama sauran yan PDP nan dake majilisar dattawa su dawo shekar APC shi yasa nayi maka wannan tambayar?
‘’A wannan mu idan zasu dawo APC jamiyya ce wanda kofar ta a bude ai nima da ina PDP na dawo APC nazo na tsaya zaben takaran sanata to kuma idan har koda ma duk yan PDP suce yau zasu dawo su bar yin adawa su dawo APC kofar APC a bude take sabo da haka wannan bangaren da kike Magana ba abu wanda za ace ba zai yiyu ba, amma duk cikin siyasa idan kayi mai rinjaye yakamata ka shirya cewa wata rana zaka zamo ba kaine mai rinjaye ba kamar yadda ya kasance yanzu haka kuma idan mutum ya shiga zabe dole ka shiga da sanin cewa a cikin abu biyu daya zai faru ko kaci ko fadi’’.
Ina gaskiyar labarin da muka samu cewan tsohon shugaban majilisar dattawa David Mark an rantsad dashi a matsayin shugaban masu rinjaye a majilisar dattawa?
‘’A’a wannan ba haka bane wato abin da ya faru a zaman shugaban mu na majilisar dattawa wanda ya wuce na 7 din da aka zo kuma yana cikin majilisar dattawa na 8 kuma ba shine shugaban majilisar dattawa ba akace ya kamata a bashi mutunci da martaban a rantsar dashi shi kadai tunda yayi shugabancin wannan majilisar ‘’
Akwai korafe-korafen da muka samu cewa a majilisar dattawan nan ba a rantsar daku ba kafin ayi zaben shugabanni hakan na yiyuwa?
‘’A’a dama baa yin haka zabe mutum biyu ne ake zaba a zaman shugabani Presiding officers ake cewa da shugaban majilisar dattawa za a fara sannan ayi mataimakin sa kuma haka akayi kuma bayan an gama wannan shine za a rantsad da sauran gaba daya.’’
Your browser doesn’t support HTML5