Tsokacin Masana Shari’a Kan Ba Da Belin Maryam Sanda

Alamar ma'aunin shari'a

Alamar ma'aunin shari'a

Sa’oi kadan bayan da kotun tarayya ta ba da belin Maryam Sanda, matar da ake tuhuma da kashe mijinta, Bilyaminu Bello a Abuja, babban Birnin Najeriya, masana shari’a sun fara fashin baki kan wannan hukunci.

Masana Shari’a a Najeriya Sun fara tsokaci kan hukuncin ba da belin Maryam Sanda da wata kuton tarayya ta yi a Abuja a shari’ar da ake zarginta da kashe mijinta.

A watan Nuwambar bara, aka kama Maryam bisa zarginta da kashe mai gidanta, Bilyaminu Bello.

Wata kotun tarayya da ke zama a Abuja ce ta ba da belinta kamar yadda jaridun Najeriya da dama suka ruwaito.

Tuni dai wannan mataki da kotun ta dauka ya haifar da cece-ku-ce a tsakanin masu bibiyar wannan shari’a kan ko ya dace a ba da belin mutumin da ake zargi da aikata kisan kai.

“Abinda mutane ya kamata su fahimta shi ne, zargi ko wane iri ne, ba zai zama laifi ba, sai har inan tabbatar da laifin a gaban kotu, sannan akwai sharudda da ake shimfidawa da za a bi wajen tabbatar mutum na da laifi.” Inji Barrister Zubairu Na Mama, lauya mai zaman kansa.

Barrister Na mama ya kara da cewa “kai kawon da ake yi ne wajen shari’ar da kuma shayarwa da take yi, ake son a dan takaita mata wahala, har sai an tabbatar da laifin akanta, domin yanzu ana matsayin zargi ne.”

Shin Sai Maryam Ta Kammala Rainon Ciki Da Shayar wa Kafin Hukunci Ya Hau Kanta Idan An Same Ta Da laifi?

Idan har an same ta da laifi (a wannan yanayi) akwai kebabbun wurare da za ta zauna cikin lumana cikin kulawa da ma’aikatan asibitin gidan kaso za su rika ba ta, har ta sauka lafiya.” Lauyan ya ce

Ina Fargabar Da Wasu Ke Yi Nuna wa Cewa Shari’ar Ta Dakko Shiririce wa Kenan Tun Da An Ba Da Belinta?

“Gaskiya jama’a su yi hattara, su kuma sa hakuri, kotu tana ayyukanta ne bisa ka’idoji da dokokin kasa, a ba kotu lokaci a ga me za ta yi. Zargin Kisa da ake yi."

Mai shari’ar Yusuf Halilu ne ya ba da belin Maryam a yau Laraba, bisa sharadin cewa sai ta gabatar da mutane biyu da suka mallaki kadarori a Abuja.

Sannan kotun ta bukaci mahaifin Maryam ya saka hanu akan ya amince cewa zai rika gabatar da ita a gaban kotun a duk lokacin da aka bukaci ganinta.

Maryam Sanda, ‘ya ce ga tsohuwar shugabar bankin Aso Savings, Maimuna Aliyu.

Saurari cikakkiyar hirar Nasiru Adamu El Hikaya da Barr. Zubair Na Mama:

Your browser doesn’t support HTML5

Tsokacin Masana Shari’a Kan Ba Da Belin Maryam Sanda - 5'21"