Ita dai tsohuwar 'yar Jaridar na da matukar kima a idon al'umma musamman Hausawa da ma shugabanin su dake cikin masarautu ko gwamnatoci.
shirin da Jamila ta gabatar na bankado wuru-wurun shugabanin siyasa da aka gabatar a gidan radiyon BBC din yayi matukar suna da kuma karbuwa a wajen jama'a.
Shirin da ta Kira da BBC a Karkara, a inda ta ja tawagar ma'aikatan BBC din ba dare ba rana wajen, shiga kauyaku don ganin ayyukan da 'yan siyasa ke yiwa jama'arsu ko kuma a'a.
Musamman ma 'yan siyasar da ke murkushe kudaden da aka ba wa mazabunsu don yiwa wadanda suke wakilta ayyukan ci gaba. Wakilinmu Nasiru Adamu El-Hikayah daga Abuja ya garzaya hukumar EFCC da aka ce anan aka tsareta.
Inda aka tabbatar masa da damke kwararriyar tsohuwar 'yar jaridar, sannan aka fada masa cewa ana zarginta ne da wasken sayen wani gida a Abuja da ya kai Naira Miliyan Dari Da Hamsin tare da bi da kudin ta wani kamfanin da ake zargin shima nata ne.
Wannan abu ya faru ne a lokacin da take shugabar hukumar raba filayen babban birnin tarayya a Abujar Najeriya. Ga rahoton wakilinmu a makalar sautin kasa.
Your browser doesn’t support HTML5