Abun kamar almara, ko kuma yadda masu hikimar magana kance “Ba zai taba sabuwa ba, wai Bindiga a ruwa” Ernestine Shepherd, mai shekaru tamanin da daya 81, da haihuwa na cikin koshin lafiya da annashuwa.
Amma babban abun mamaki shine, ta lashe kambun mace daya tillo a tarihin duniya da ta shiga littafin kundin abubuwan ban mamaki a duniya ‘Guinness World Records’ itace mace da ke da yawan shekaru kuma tana atisayen motsa jiki wanda ake kira ‘Bodybuilder’ a turance.
Ta bayyanar da cewar yayar ta itace wadda ta bata kwarin gwiwa wajen ganin ta shiga tarihin duniya, inda tafara motsa jiki tun tana da shekaru 56, wanda a lokacin take fama da matsalar kiba, wanda mijin ta ya umurceta da ta fara motsa jiki ko ta samu ta rage kiba, jikinta yayi kyau.
Hakan ya taimaka mata matuka, domin kuwa takan fita don gudu a kowace safiya, kana takan je wajen motsa jiki na awowi biyu da rabi a cikin kwanaki uku na sati. Kocin ta ya taka rawar gani wajen ganin batayi kasa a gwiwa ba.
Domin kuwa yana bata duk gwarin gwiwa da ya kamata ace ta samu don cika burinta, har ma yakan gaya mata cewar “Shekaru ba wasu abu bane illa lambobi, don haka kada kitaba tunanin cewar bazaki iyayi ba don wai kin tsufa”
Ta cigaba wanda da rana tsaka sai ka ma’aikatan hukumar kundin tarihin abubuwan duniya, sun kirata da cewar itace mace mafi yawan shekaru kuma tsohuwa dake atisayen gina jiki, amma suna so su tabbatar da hakan kamin su bata kambun.
Ta samu wannan karramawar na rike wannan kambun har na tsawon shekaru biyu, tana ba mata musamman masu shekaru shawara da su dinga motsa jiki, ko hakan ya kara musu yawan shekaru cikin koshin lafiya.
Sai ta kara da cewar "idan akwai maganin tsufa, to ba wani abu bane da ya wuce atisaye a kowane lokaci, da cin abinci mai gina jiki"