Murtala Sanyinna yace a lokacin da yake zagayen ganin yadda zabe yake tafiya inda har garin Jega ya zagaya, ya kuma kama hanyarsa ta zuwa Birnin Kebbi. To a wani kauye a karamar hukumar Kalgo dake kan hanyar zuwa birnin kebbin sai ya tsaya don ganin yadda nan ma zaben ke tafiya.
To a nan ne fa yaga abin mamaki. Inda yace wata tsohuwa ‘yar kimanin shekaru 70 zuwa 75 ta zo zata yi zabenta. Sai aka bata takardun kada kuri’a guda uku, na ‘yan majalisun tarayya, dana dattawa da kuma ta shugaban kasa. Da tsohuwar nan ta karba sai ta garzaya inda ake dan buya a dangwalawa zabin da aka yi ta zaba ta fito.
Bayan fitowarta sai ta je don kokarin jefa wa a inda aka tanada. To sai jami’in zaben wajen ya dan lura da kamar akwai dan tangarda. Nan suka karba suka duba, inda suka gag aba daya ta dangwale gidajen dangwala zabin na mutumin da ake son zaba.
Sai jami’in zabe yace mata ai kin bata takarda taki dattijuwa. Sai tsohuwa tace a’a ita bata bata komai ba domin kuwa ta yi abinda Buhari yace su yi ne. Da jami’in ya tambayeta me Buharin yace ku yi? Sai tace, Buhari yace mu dangwalawa APC daga sama har kasa, kuma abinda nayi Kenan. Haka dai karshe dole aka kyaleta ta gama ta tafi abinta.