An bai wa tsohon shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe da matarsa Grace rigar kariya da za ta hana a tuhume su.
Wani jami’in jami’ya mai mulki ta ZANU-PF, da kuma wani dan jarida ne suka tabbatar wa da Muryar Amurka hakan a jiya Alhamis.
Mugabe yana ta ganawa da Janar-janar din soji da kuma shugabannin siyasar kasar, wadanda suka tilasta mai ya yi murabus a ranar Talata, kan yadda zai yi ritaya, bayan da ya kwashe shekaru 37 yana mulki.
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama, sun zargi Mugabe da murde zabukan kasar, da yin facaka da kudaden kasar da kuma zargin cewa yana da hanu a kisa da azabtar da dubban abokanan hamayyar siyasarsa a tsawon lokacin da ya kwashe yana mulki.
Kakakin Majalisar dokokin kasar, ya ce a yau Juma’a za a rantsar da tsohon mataimkin shugaban kasar, Emmerson Mnangagwa, a matsayin sabon shugaban kasar Zimbabwe.