Wannan shine hukuncin farko da aka yanke a jerin tuhume-tuhume da ake yiwa al-Bashir, wanda kuma kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ke nemansa kan laifukan yaki da kisan kare dangi dake alaka da tashin hankalin da ya faru a Darfur a shekarun 2000.
Hukuncin na zuwa ne shekara guda bayan da masu zanga-zanga a Sudan suka fara yiwa gwamnatin al-Bashir tawaye. Lokacin da ya kwashe sama da shekaru talatin akan mulki, Sudan dai ta kasance cikin jerin kasashen da Amurka ke dauka a matsayin masu tallafawa ayyukan ta’addanci a duniya, kuma tsawon shekaru tattalin arzikin kasar ya lalace saboda rashin gudanar da ayyyukan da suka kamata da kuma takunkumin da Amurka ta saka ma kasar.
Tun watan Afrilu Al-Bashir ke tsare, lokacin da sojojin suka tunbuke gwamnatinsa biyo bayan kwahe watanni ana zanga-znaga a fadin kasar. Sannu a hankali tashin hankali da rashin zaman lafiya ya tilasta yarjejeniyar gudanar da gwamnati tsakanin sojoji da farar hula.