Tsohon shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka Steve Lucas ya rasu.
Marigayi Lucas ya rasu ne a jihar Florida da ke Amurka bayan fama da rashin lafiya. Shekarunsa 75.
Lucas ya kwashe shekaru sama da 20 yana aiki a Muryar Amurka (VOA,) inda ya fara a matsayin mai neman labarai, sannan daga baya ya zama shugaban Sashen Hausa.
Daga baya Lucas ya zama Darekta a shiyyar Afirka na Muryar Amurka mai kula da sassan watsa labaru cikin harsuna takwas.
Daga nan ne kuma aka mayar da shi Darektan ofishin kafawa tare da inganta hulda da gidajen watsa labarai na kasashen yammacin Afirka.
Ya rike wannan mukamin har zuwa lokacin da ya yi ritaya a shekarar 2008, inda daga nan ya koma jiharsa Florida.
Ya ci gaba da zama a jihar ta Florida tare da uwargidansa Fatima da diyarsa Zainab.
A wani mataki da ya dauka don kada ya manta da harshen Hausa kamar yadda ya taba fada a wata hira da aka yi da shi, Lucas ya fara aiki da Sashen Hausa na Radio France (RFI) inda yake aika musu rahoto daga Florida.
Marigayi Lucas kwararre ne fannin sarrafa harshen Hausa. An haife shi ne a garin Vom da ke karamar hukumar Jos ta kudu a jihar Filaton Najeriya a lokacin da iyayensa suka je aiki a yankin.
Sannan ya kwashe shekaru da dama a Jamhuriyar Nijar a lokacin da iyayensa suka koma aiki a kasar inda suka gina asibitin kutare.