Tsofaffin shugabannin Nigeria guda biyu da suka hada Goodluck Jonathan tsohon shugaban Najeriya da Janar Ibrahim Badamasi Banagida, sun yi ganawar sirri a Minna, fadar gwamnatin jihar Neja.
Bayan taron na wajen awa biyu da rabi babu wani cikakken bayani da aka bayar. Shi ma tsohon shugaba Jonathan ya ki ya ce uffan ma manema labarai koda yake ya ce ya zo gaida Janar Babangida ne.
To sai dai masu lura da al’amuran siyasa na ganin ziyarar Jonathan ba zata rasa nasaba da babban zaben jam’iyyar PDP dake tafe ba, kamar yadda daya cikin shugabannin jam’iyyar a Neja, Yahaya Ability, ya bayyana. Ya ce taron ba zai rasa nasaba ba da babban taron zaben jam’iyyar da za’ayi ranar 9 ga watan Disambar wannan shekarar da kuma tabattarda ganin anyi shi a cikin lumana.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5