Ga dukkaan alamu, hukuncin da aka yanke wa tsohon shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva na zaman gidan yari har na tsawon shekaru 9.5 bai ga bayan shari'ar da ake yi wa tsohon shugaban kasar ba.
Da Silva ya bayyana cewa zai daukaka kara bisa wannan hukuncin domin tabbatar da gaskiyarsa.
Shugaban da aka fi saninsa da Lula, ya musunta zargin da ake masa na karbar sama da dalar Amurka miliyan daya daga wani kamfanin domin kayata wani gidansa dake gabar ruwa.
Alkalin kotun tarayya Sergio Moro ya samu mashahurin dan siyasar da laifin karban kudaden.
Wannan na cikin batutuwan rashawa da dama da ake bincike a kai, wanda ya mayar da hankali a kan babbar ma’aikatar mai ta kasar ta Petrobas wanda ya kai ga daure shugabannin kasuwanci da 'yan siyasa.