Tsohon Shugaban Amurka Jimmy Carter Ya Rasu

 Jimmy Carter ne shugaban kasar Amurka na farko da ya kai shekara 100 a duniya.

A yau Lahadi tsohon Shugaban Amurka, Jimmy Carter ya mutu yana da shekara 100.

Wata sanarwa da gidauniyarsa ta fitar ta ce shugaban Amurka na 39 ya rasu a gidansa da ke tsaunin Plains da ke jihar Georgia a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

An zabe shi a matsayin shugaban Amurka a shekarar 1976 ya kuma hau karagar mulki a shakar 1977 zuwa 1981.

Jimmy Carter ne shugaban kasar Amurka na farko da ya kai shekara 100 a duniya.

Rana 1 ga watan Oktoban shekarar 1924 aka haife shi a tsaunin Plains da ke birnin Georjiya inda ya ci gaba da tarewa bayan cire hannunsa daga siyasa a shekarar 1981.