Yanzu a hannun EFCC dake Abuja babban birnin Najeriya, akwai tsohon karamin ministan tsaro Obanikoro da tsohon kakakin kemfen din Goodluck Jonathan Femi Fani-Kayode.
Wadanda aka kama da can sun dawo da makudan kudade ko kuma an kwato kudaden almundahana daga hannunsu. An rufe ma wasu daga cikin gidajensu da bincike ya nuna an ginasu ne ko an sayesu da kudin zarmiya.
Babban abun da ya fi damun jama'a shi ne yadda waddanda aka kama ke saurin samun beli. Kakakin EFCC yace ba ma bada belin ke kawo cikas ba illa irin yadda waddanda aka kama ke shigar da kara a kotuna.
Yanzu dai ido ya koma kan alkalai da yadda zasu taka rawa wajen yin shari'a akan almundahana da cin hanci a daidai lokacin da ake zargin wasu alkalan da hannu dumu-dumu a cin hanci da rashawa.
Modibo Zakari lauya mai zaman kansa ya kira lauyoyi 'yanuwansa da su kara hakuri su kai zuciya nesa domin ba duka lauyoyi ba ne ke goyon bayan abubuwan dake faruwa a fannin shari'a. Wasu ma na ganin wasu lauyoyi da wasu alkalai bakinsu daya. Ana ganin wasu lauyoyin ma 'yan karen farautan alkalai ne.
Alkali mai hankali da basira da wuya addini ko bangaranci ko kabilanci ko sabo su rinjayeshi wajen yanke hukumci saboda yana da rantsuwar kama aiki da kuma bin tsarin horo da sana'arsa ta alkalanci, inji Modibo Zakari
Wannan kamen ya birge wani manomi Alhaji Musa Yola wanda ya bayar da wata wasiya yana kiran a sake zabar Buhari a zabe na gaba. Yace wadanda su kayi karatu kyauta a arewa su ne suka bata kasar. Yace komi kyauta aka yi masu amma kuma su ne suka zama barayi. 'Yan shekaru 45 zuwa 65 su ne suka cuci kasar.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5