Kafin rasuwarshi, Ladan Ibrahim Ayawa ya yi aiki da Muryar Amurka na tsawon shekaru da dama, inda ya fara a matsayin wakili da ke dauko rahotanni a birnin Lagos, kafin a dauke shi aiki a shelkwatar Sashen Hausa a Washington.
Marigayi Ladan Ibrahim Ayawa wanda haifaffen jihar Naija ne, kwararren dan jarida ne wanda kafin aiki da Muryar Amurka, ya kuma yi aiki da Radio Nigeria.
Daga cikin fitattun shirye shiryen da Ladan ya gabatar akwai shirin Himma bata ga rago, shirin da ke hira da 'yan asalin kasar Afrika dake zaune a kasashen ketare.
Your browser doesn’t support HTML5
Ladan Ayawa ya kuma gabatar da shirin da ke haska fitila kan harkokin zabe a kasashen duniya musamman kasashe masu tasowa inda ake yawan zargin magudi.
Ga shirin Zabe ko nadi na karshe da ya gabatar
Your browser doesn’t support HTML5
Ladan ya rasu ya bar matarsa Talatu da kuma 'ya'ya uku, namiji daya da 'yammata biyu.
Yau ake kyautata zaton za a yi jana'izar shi a jihar Maryland bayan an yi mashi sallah a babban masallacin karamar Hukumar Prince Georges.