Tsohon Kocin Najeriya Keshi Ya Rasu

Stephen Keshi

Rahotanni daga Najeriya na cewa tsohon kocin ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles, Stephen Keshi ya rasu. Ya rasu yana mai shekaru 54.

Wata sanarwa da kakakin iyalan mamacin, Emmanuel Ado ya fitar ta yi nuni da cewa Keshi ya rasu ne da sanyin safiyar yau Laraba, bayan da ya yi fama da bugun zuciya a birnin Benin da ke jihar Edo, a kudu maso kudancin Najeriya.

Babban Sakataren kungiyar kwallon kafa ta NFF, Dr. Mohammed Sunusi ya kuma tabbatar da mutuwar Keshi.

“Labarin da muka samu shi ne ya ce yana jin kamar kafarsa tana mai ciwo, to sai aka garzaya da shi asibiti, amma kuma daga baya sai rai ya yi halinsa.” Inji Dr. Sunusi.

Keshi shi ne kocin Najeriya na farko da ya taba lashe gasar cin kofin nahiyar Afrika a matsayin dan wasa da kuma koci.

Ya kuma bugawa kungiyoyin kwallon kafa a kasar Belgium wasanni da dama gabanin ya zama kocin na Najeriya.

A watan Disambar bara mai dakin Keshi Kate ta rasu bayan shekaru sama da shekaru 30 da suka kwashe suna matsayin ma’aurata.

Kate ta rasu ne bayan da ta yi fama da rashin lafiya mai nasaba da sankara ko kuma cutar daji, lamarin da ‘yan uwa da abokan tsohon kocin su ka ce ya kada shi matuka.

Keshi ya rasu ya bar 'ya'ya hudu da mahaifiyarsa.