WASHINGTON DC, —
Bincike ya nuna cewar tsohon dan wasan Liverpool mai suna Michael Robinson, na dauke da cutar daji na fatar jiki (Skin Cancer).
Tsohon dan wasan mai shekaru 60 da haihuwa, ya buga wasanni a kungiyoyin kwallon kafa da dama, mafi yawanci kulob din a kasar Ingila wanda ya fara daga kungiyar Preston, Manchester City, Brighton da kuma Queens Park
Rangers, ya ajiye takalman wasan sane a kungiyar kwallon kafa ta Osasuna dake kasar Spain a shekara 1989.
A yanzu yana daya daga cikin masu watsa Labaran wasanni a kasar Spain. A lokacin da yake taka leda a kungiyar Liverpool, daga shekara ta 1983 zuwa 1984, Robinson ya taimakawa kulob din ta samu nasarar lashe kofin Turai (First Division) da kuma League Cup.