Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alh. Garba Nadama Ya Rasu

Alh. Dr. Garba Nadama

Da misalin karfe 7:30 na daren yau Litinin, Allah ya yi wa tsohon gwamnan farar hula na jamhuriya ta biyu Alh. Dr. Garba Nadama rasuwa a gidan shi da ke cikin birnin Sokoto.

Alh. Garba Nadama, ya rasu ya bar 'ya'ya 18, mata hudu, da jikoki da dama. Za a yi jana'izarsa gobe Talata da safe idan Allah ya kai rai. Ya rasu yana da shekaru 87 a duniya.

A shekar 1979 aka zabi margayi Alh. Shehu Kangiwa a matsayin gwamnan jihar Sakkwato na farko, wanda margayi Alh. Garba Nadama ya zama mataimakinsa, a ranar 17 ga watan Nuwambar shekarar 1981 Allah ya dauki ran tsohon gwamna Alh. Shehu Kangiwa a garin Kaduna.

An rantsar da margayi Alh. Garba Nadama a matsayin gwamnan jihar har zuwa shekarar 1983.

Margayin Alh. Garba Nadama, ya yi karatun digirin-digirgir a jami’ar Ahmadu Bello Zaria, inda yayi karatu a fannin tarihi.