Tsohon gwamnan jihar Gombe, Alhaji Habu Hashidu ya rasu bayan fama da ya yi da rashin lafiya.
Ya rasu yana mai shekaru 74.
An yi jana'izar marigayin a kofar fadar sarkin Gombe da misalin karfe 5 na yamma a yau Juma'a 27 ga watan Yulin shekarar 2018.
An haife shi a garin Hashidu da ke karamar hukumar Dukku a jihar ta Gombe a ranar 10 ga watan Afrilun shekarar 1944.
Marigayin ya yi ayyuka da dama a zamanin tsohuwar gwamnatin jihar arewa maso gabas a ma'aikatar gona da albarkatun kasa, a yayin da ya taba rike mukamin kwamishinan ayyukan gona a tsohuwar gwamnatin jihar Bauchi.
Har ila yau taba rike mukamin ministan albarkatun ruwa da kuma ministan ayyukan gona da bunkasa yankunan karkara a mulkin soja na shugaba Ibrahim Babangida inda daga nan ne ya yi ritaya.
A shekarar 1999 marigayi ya yi takarar kujerar gwamnan jihar gombe a karkashin jam'iyar APP ta da inda ya yi mulki daga shekarar 1999 zuwa 2003.
Habu Hashisu ya rasu ya bar mata daya da yara takwas maza uku mata biyar.