Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido Yace Kowa Nada ‘Yancin Tsayawa Takara

  • Ladan Ayawa
Jigawa State Governor Sule Lamido (R) waits on set for interview to begin.

Jigawa State Governor Sule Lamido (R) waits on set for interview to begin.

Tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido yace duk wani dan Najeriya nada 'yancin tsayawa takara kuma 'yan Najeriya sune zasu yanke hukunci

Tsohon gwamnan yana Magana sailin da yake amsa tambayoyin ‘yan jaridu game da kalaman tsoffin shugabanin Najeriya wato Janar Olusegun Obasanjo da Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Idan dai ba a manta ba shugabannin biyu sun rubuta wasika ga shugaba Muhammadu Buhari suna bashi shawara,duk da yake shugaba Ibrahim Badamasi Babangida yace baice kar shugaba Buhari ya tsaya takara ba.

Sai dai a zantawar da ‘yan jarida suka yi da tsohon gwamnan jihar na Jigawa Alhaji Sule Lamido, yace tsarin mulkin Najeriya, mutane suna a ‘yancin suyi zaben su.

Yace akwai jamiyyu a Najeriya da suka kai sama da 50, duk wata jamiyyar dake son tasa matasa domin takara tana iya yin hakan wannan ba laifi bane.

Hukuncin zaben waya dace da ya mulki Najeriya, wannan abu ne da saisu ‘yan Najeriya ne kadai zasu iya yanke wannan hukuncin.

Ga Mahmud Kwari da Karin bayani.3’34