Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa Tsohon Firai Ministan Jamhuriyar Nijar Hama Amadou ya rasu.
Amadou wanda har ila yau tsohon Kakaki ne a Majalisar Dokokin Nijar ya rasu ne a birnin Yamai bayan fama da rashin lafiya.
A bara ne Amadou da ke hijira a kasashen waje ya koma gida da nufin ba da gudunmowa a kokarin fitar da kasar daga dambarwar siyasar da ta biyo bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.
A yayin da magoya bayansa ke cewa zai taimaka a shayo kan takun sakar da ke tsakanin kasar da kungiyar ECOWAS wasu kuwa sun bukaci madugun ‘yan hamayyar ya kai kansa mashara’anta saboda laifukan da ake zargin ya aikata a baya.
Amadou ya shafe shekaru biyu a tsakanin Faransa da sauran kasashen duniya cikin wani yanayin da ke kama da gudun hijira mai nasaba da matsalolin da ya fuskanta a zamanin da shudediyar gwamnati.
A shekarar 2013 gwamnatin shugaba Issouhou Mahamodu ta zarge shi da laifin sayen jarirai daga Najeriya inda ya arce daga Nijar a watan Agustan 2014 jim kadan bayan da kwamitin jagorancin majalisar ya cire masa rigar kariya a wani shirin gurfanar da shi a gaban kotu.
Bayan dawowar shi gida a shekarar 2016 da 2020 madugun ‘yan hamayyar ya bakuncin kurkuku a washegarin zaben 2021 saboda zarginsa da yunkurin ta da zaune tsaye.
Saurari rahoton Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5