Tsohon dan wasan gaba na kasar Ajantina Diego Maradona, ya dawo bakin aikinsa na horas da kungiyar kwallon kafa ta Gimnasia, mai buga wasan lig a kasar Ajantina.
A farkon wannan makon ne kocin mai shekaru 59 da haihuwa, yace ya ajiye aikinsa a kungiyar Gimnasia, kwanaki biyu kacal ya kuma sake wallafawa a shafinsa na sada zumunta cewar ya dawo bakin aiki.
Maradona ya kama aiki a kulob din ne a farkon watan Satumbar 2019, watanni uku kenan.
Kocin ya ce sun samu dai-dato da mahukuntar kungiyar, don haka shi yasa ya dawo don cigaba da aikin horas da 'yan wasan kungiyar.
Ya kuma ce yana fatan shugabannin kulob din za su samar da abubuwan karfafa gwiwa, kamar yadda suka masa alkawari domin kawo cigaba.
Maradona wanda ya lashe kofin duniya na 1986, lokacin yana dan wasa a kasar Ajantina, ya kuma ja ragamar horas da kungiyoyin kwallon kafa daban daban, kungiyar da ya horas a karshe ita ce Dorados ta kasar Mexico, wanda ya barta saboda rashin lafiyar da yake fama dashi a lokacin.
A yanzu haka kungiyar da yake jagoranta Gimnasia tana mataki na 22 a lig din bana, inda yayi nasara a wasanni uku kacal cikin takwas da ya jagoranta.