Tsohon Dan Wasan Everton Li Tie, Ya Zama Kocin Kasar China

Tsohon dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Everton Li Tie, ya zamo sabon kocin kasar China.

Tie, mai shekaru 42 da haihuwa, ya maye gurbin Marcello Lippi, wanda ya ajiye aikinsa bayan da kasar China ta sha kashi a hannun Syria da ci 2-1, inda ta gaza samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya na 2022.

Sabon kocin Tie ya buga wasannin 92 ga kasar ta China a lokacin da yake fafata wasa.

Ya kasance daya daga cikin 'yan wasan da suka halarci gasar cin kofin duniya a shekarar 2002.

A shekara ta 2002 ya bugawa Everton, ya buga wasanni 40 a karkashin jagorancin David Moyes, daga bisani ya koma Sheffield United a 2006.

A shekarar 2011, ya rataye takalman wasansa ya zamo kocin kungiyar kwallon kafa na Guangzhou Evergrande, da kuma Hebei Fortune sannan Wuhan Zall.