Tsohon Dan Majalisar Tarayyar Najeriya Farouk Lawan Ya Shaki Iskar 'Yanci

Farouk Lawan

An sako shi daga gidan yarin kuje na Abuja ne bayan da ya shafe shekaru a gidan kaso, a yau Talata.

Tsohon dan Majalisar Wakilai Farouk Lawan ya shaki iskar 'yanci bayan da ya shafe shekaru 5 a gidan yari saboda nema da karbar cin hancin dala dubu 500 daga attajirin dan kasuwa Femi Otedola.

An sake shi daga gidan gyaran hali na kuje dake Abuja ne a yau Talata.

"Yau an bude sabon babi a rayuwata yayin da nake fita daga gidan gyaran hali na Kuje, ina mai matukar godiya ga Allah daya fidda ni daga wannan kangi," a cewar sanarwar daya fitar a yau.

Tsohon dan najalisar ya kuma godewa 'yan uwa da abokan arziki game da tallafawarsu a wannan lokaci na iftila'i a rayuwata."

"Ina matukar godiya, gashi ina raye cikin koshin lafiya da karsashin da zan kasance da 'yan uwa da abokai da dangina, bana daukar hakan da wasa," a cewarsa.

"Ba zan manta da gudunmowar da 'yan uwa da abokai suka bayar a wannan lokaci na iftila'i a rayuwata ba."

An same Lawan, wadda tsohon shugaban kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai kan tallafin man fetur ne, da laifi kuma aka yanke masa hukuncin dauri zuwa gidan yari a shekarar 2021.