Tsofaffin Sojoji Sun Mamaye Ma’aikatar Kudin Najeriya

Gamayyar Sojoji ‘Yan fansho dake Abuja sun mamaye ma’aikatar kudi ta tarayyar Najeriya

Tsofaffin sojojin da suka yi ritaya karkashin inuwar Gamayyar Sojoji ‘Yan fansho dake Abuja sun mamaye ma’aikatar kudi ta tarayyar Najeriya da safiyar yau alhamis akan rashin biyansu kaso 20 zuwa 28 cikin 100 na karin albashin da aka yi daga watan Janairu zuwa Nuwamban 2024.

Tsaffin sojojin da suka hallara daga rassan kungiyar daban-daban sun koka akan gazawar gwamnatin tarayya wajen biyansu hakkokinsu.

Gamayyar Sojoji ‘Yan fansho dake Abuja sun mamaye Ma’aikatar Kudi ta tarayyar Najeriya

Bukatun tsaffin mazan jiyan sun hada da biyan kudaden tallafi daga watan Oktoba zuwa Nuwamban 2024 da biyan Naira 32, 000 da aka kara a kan kudaden fansho, da biyan alawus din killacewar tsaro (SDA) a dunkule da kuma dawo da kudaden da aka yanka da fanshon sojojin dake da larurar rashin lafiya.

A watan Disamban 2023, Majalisar Dattawa ta bayyana shirin gudanar da cikakken bincike a kan hukumar dake kula da fanshon sojoji.

Shugaban kwamitin fanshon sojoji na majalisar ya tuhumi yadda hukumar ke gudanar da ayyukanta, da kasafin kudinta da kuma adadin ‘yan fansho da aka bada rahoton sun karbi hakkokinsu.